Bangaren kasa da kasa: An gudanar da wani zaman taro a birnin (Wujdah) na kasar Morocco kan illimomin addini da kuma harshen larabci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga daga shafin internet na (Le matin) cewa; an gudanar da zaman taro a birnin Wujdah na kasar Morocco dangane da matsayin ilmomin addini da kuma rawar da harshen larabci ke takawa wajen yada wadannan ilmomi. Bayanin ya ce malaman jami'a gami dam asana daga sassa daban-daban na kasar da ma wasu kasashen ketare musamman ma na larabawa sun halarci zaman taron, inda suka tattauna muhimman batutuwa da suke da dangantaka da ilmomin addini da kuma irin gundunmawar da za su iya bayarwa wajen ilmantar da al'umma domin kyautata zamantakewa, da kuma ilmantarwa a addinance, gami da karfafa ilimin yaren larabci, domin kuwa daga cikin abubuwan da mahalartan suka hadu kansa har da karfafa karatun kur'ani, gami da sauran ilmomin addinin Musulunci, wanda hakan ke bukatar masaniya kan yaren larabci.
374520