IQNA

An Ware Dalar Amurka Miliyan 25 A Kasar Qatar Domin Buga Kur'ani

18:16 - March 09, 2009
Lambar Labari: 1753958
Bangaren kasa da kasa: Ma'aikatar kula da harkokin Musulunci a kasar Qatar ta sanar cewa ta ware makudan kudi har dalar Amurka miliyar 25 domin buga kur'ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Peninsula) cewa; babban jami'i mai kula da ma'akatar harkokin addinin Musulunci a kasar Qatar Mohammad Saleh a wata zantawa da ta hada shi da jaridar (Al-sharq) ta kasar Qatar ya bayyana cewa; ya zuwa yanzu sun ware kudi kimanin dalar Amurka miliyan 25 domin buga wani alkur'ani da aka rubuta a kasar, wanda ya kebantu da salon rubutu na musamman, ta fuskacin kayatrwa da tsari, wanda tuni jami'ar Azhar ta baiwa kasar Qatar damar buga wannan kur'ani, wanda kuma za a yada a duniya.
Ya ce bugun farko zai kai kur'ani dubu 700, wanda ya aka raba shi shi zuwa mujalladi 5, kuma ana sa ran nan da 'yan kwanaki za a kammala aikinsa

374657

captcha