IQNA

Kasashen Musulimi Na Kokarin Fadada Rawar Da Mata Ke Takawa

16:22 - March 10, 2009
Lambar Labari: 1754300
Bangaren kasa da kasa: Kungiyar bunkasa da ilimi da al'adun Musulunci ta sanar cewa ya kamata kasashen musulmi su baiwa mata damar taka muhimmir rawa a cikin al'umma.
Kamfanin dillancin Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (Kuna) cewa; kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun Musulunci ta kirayi kasashen musulmi da su baiwa mata damar taka muhimmar rawa a cikin rayuwar al'umma ta yau da kullum, da hakan ya hada da bangarori na tattalin arziki al'adu da dai sauransu.
Kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun Musulunci ta sanar da hakan ne a cikin wani bayani da ta fitar jiya, bayan kammala wani zama da ta gudanar dangane da irin rawar da mata za su iya bayarwa wajen gina gina ta fuskoki da dama, inda bayanin ya jaddada wajibcin kula da ilimin mata a dukkanin fagage.

375232



captcha