IQNA

A Gudanar Da Taron Mauludi A Garin Qirwan Na Tunusia

16:21 - March 10, 2009
Lambar Labari: 1754301
Bangaren kasa da kasa: An gudanar da taron Mauludi a garin Qirwan na kasar Tunusia, domin murnar tunawa da zagayowar haihuwar ma'aiki (SAW)
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (TAP) cewa; an gudanar da taron mauludi a birnin Qirwan na kasar Tunusia, kuma an gudanar da taron ne a masallacin nan mai dogon tarihi na (Oqba Bin Nafi) inda taron ya samu halartar malaman addini daga sassa daban-daban a fadin kasar ta Tunusia, da kuma shugabannin kungiyoyin addini da na siyasa gami da wasu jami'an gwamnati, kamar yadda taron ya samu halartar wakilai daga kungiyar bunkasa ilimi da al'adun mulunci, gami da wasu malamai daga wasu kasashen nahiyar Afirka musamman daga arewaci da yammacin nahiyar.

375318

captcha