IQNA

An Yada Littafin Share Fage Na Koyar Da Karatun Kur'ani A Rasha

Bangaren al'adu Fasaha: An buga tare da yada littafin share fage na koyar da karatun kur'ani a kasar rasha mai suna (malami na biyu) a cikin shafuka 128.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa wannan littafi an tsara shi ta hanya mai sauki da za ta koyar da karatun kur'ani cikin sauki, bugu da kari kuma littafin bai takaitu da koyar da kira'a ba kawai, a'a har ma da fahimtar da mai karatu ma'anonin abin da yake karantawa na ayoyin ubangiji madaukakin sarki.
Duk da cewa littafin an rubuta shi ne a cikin harshen rashanci, amma kuma a lokaci guda yana koyar da wasu kalmomi na larabci wadanda suka zo a cikin kur'ani mai tsarki wadanda sukebukatar karin haske, da hakan ya hada sanin kalmomin acikin lugga, da kuma yadda ake yin amfani da su a cikin isdilahi, kuma madaba'antar nan ta rasha Ilia ita ce ta dauki nauyin buga tare dayada littafin.

374893