IQNA

An Gudanar Da Taro Kan Al'adu Da Likitanci A Musulunci A Iran

Bangaren al'adu da fasaha: Jami'ar koyon aikin likitanci da harhada magunguna ta Shahid Beheshti, ta gudanar da wani taro a karon farko kan kan al'adu da kuma likitanci a Musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa: reshen ma'aikatar ilimi da bincike da ke jami'ar koyon aikin likitanci da harhada magunguna ta Shahid Beheshti, gami da hadin gwiwa da mahukuntan jami'ar ya gudanar da wani taro kan al'adu da kuma aikin likitanci da aka gada a Musulunci, gami da irin rawar dam asana Iraniya suka bayar a tsawon tarihi wajen bunkasa wannan ilimi.
Rahoton ya ce wannan shi ne karo na farko da aka gudanar da irin wannan taro, wanda ma'aikatar kula da al'adu ta Iran da kuma ma'aikatar kiwon lafiya suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen gudanar da shi, wanda ya kayatar da dukkanin mahalarta kama daga dalibai har zuwa manyan jami'an gwamnati da aka gayyata zuwa wajen taron.

375330