IQNA

An Yi Bayani Kan Manzon Allah (SAW) A Mahangar Jagora

Bangaren Zamantakewa: Jami'ar Shahid Chamran ta fitar da wani littafi mai suna (Bahara) da ke bayani kan ma'aiki a mahangar jagoran juyin juya halin Musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; reshen jami'ar Shahid Chamran da ke birnin Ahvaz babban birnin lardin Khuzestan, ya fitar da wani littafi mai suna (Baharan) wanda ya yi bayani kan ma'aiki (SAW) a mahangar jagoran juyin juyin halin Musulunci a Iran. Inda littafin ya kawo muhimman abubuwa da ya kamata musulmi ya yi kyakkyawan la'akari da su dangane da rayuwar ma'aiki, wanda kuma shi ne babban abin koyi ga musulmi a cikin dukkanin rayuwarsa. Reshen jami'ar na Ahvaz ne ya dauki nauyin buga littafin tare da kaddamar da shi da kuma yada shi.

371582