Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Islam online) cewa; malamin addinin Musulunci dan kasar Malawi (sheikh Aman Kingambeh) ya sheda wa shafin cewa sun aike da takardar gayyata ga mabiya addinin kirista na kasar zuwa ga taron maulidin manzon Allah (SAW) kuma sun karba wannan goron gayyata, inda suka halarci taron mauludi da musulmi suka gudanar a kasar.
Malamin ya kara da cewa; wannan goron gayyata da suka aike wa mabiya addinin kirista zuwa ga taron maulidi ya tabbatar da cewa addinin Musulunci addini ne na zman lafiya, tare da karfafa fahimtar juna tsakaninsa da sauran addinai, kuma karba goron gayyatar ya tabbatar da cewa al'ummar musulmi da kirista a kasar Malawi suna zaman lafiya ne da junansu.
375904