IQNA

An Gudanar Da Taron Maulidin Annabi (SAW) A Chechnia

15:20 - March 11, 2009
Lambar Labari: 1754944
Bangaren kasa da kasa: An gudanar da babban taron maulidin Annabi (SAW) a birnin Grozni na Chechnia, wanda ya samu halartar mutane da dama.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Faransa (La Croix) cewa; an gudanar da babban taron maulidin manzon Allah (SAW) a babban masallacin juma'a na birnin Grozni fadar mulkin Chechniya, wanda ya samu halartar shugaban jamhuriyar Chechniya (Ramadan Qadiruv) da kuma shugaban Ingushitia (Bek Evkourov) gami da wasu musulmin chechniya da aka kaddara yawansu da mutane dubu 20.
Shugaban Jamhuriyar Chechniya ya gabatar da jawabi a wajen taron maulidin, inda ya bayyana cewa a 'yan shekarun da suka gabata akidar wahabiyanci ta fara bazuwa a cikin yankunan Chechniya, amma halartar da dubban musulmi suka yi wajen taron maulidin manzon Allah (SAW) ya tabbatar da cewa akidar wahabiyanci a halin yanzu ba ta da wurin zama a tsakanin al'ummar kasar masu son manzon rahma (SAW).

375863



captcha