IQNA

An Gudanar Da Taron Hadin Gwiwa Kan Shirye-Shiryen Kur'ani

15:10 - March 11, 2009
Lambar Labari: 1754945
Bangaren kasa da kasa: An gudanar da zama na biyar karkashin kwamitin hadin gwiwa kan shirye-shiryen kur'ani wajen Iran wanda za a aiwatar a cikin shekara ta 1388 hijira shamsiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; an gudanar da zama karo na biyar kan kan batun shirye-shiryen kur'ani da a ke gudanarwa a wajen Iran, wanda shugaban kwamitin da ke kula da wadannan ayyuka ne (mahmud Wa'izi) ya jagoranci gudanar da zaman, wanda ya yi dubi kan muhimman abubuwan da ya kamata a mayar da hankali kansu dangane da shirye-shiryen kur'ani a wajen Iran.
A lokacin gudanar da zaman taron ya kabayyana cewa; shirye-shiryen da ake gudanarwa a halin yanzu a fagen kur'ani a karkashin kwamitin a kasashen duniya na bukatar karin fadada, musamman idan aka yi la'akari da irin bukatuwar da ake da ita ga ayyukan wannan kwamiti, domin kuwa al'ummomin musulmin a duniya na kishirwar shirye-shiryen da za su taimaka musu wajen sanin kur'ani mai tsarki, wanda kuma hakan shi ne babban aikin wannan kwamiti, ya ce za su mayar da hankali wajen safke nauyin da ya rataya kansu.

375665





captcha