Bangaren da ke wakiltar Qods Razavi: Shugaban bangaren da ke kula da isar da sakonni da kyautata alakar Musulunci a cibiyar Imam Rida ta Qods Razavi, ya bayyana cewa za a gudanar da tarukan maulidin manzon Allah (SAW) a hubbaren Imam Rida (AS).
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Shugaban bangaren da ke kula da isar da sakonni da kyautata alakar Musulunci a cibiyar Imam Rida ta Qods Razavi, ya bayyana cewa za a gudanar da tarukan maulidin manzon Allah (SAW) a hubbaren Imam Rida (AS) ya ci gaba da cewa wasu daga cikin malamai za su gabatar da jawabai kan maulidi da kuma fadakar da jam'a kan hikimar da ke tatatre da hakan, da kuma hanyoyin da za a bi wajen koyi da manzon Allah (SAW) a cikin dukkanin ayyuka na rayuwa.
Daga cikin malaman da za su gabatar da jawabai a wajen taron taron maulidin akwai (Jamali) da kuma (Taqviyan) kuma a ranar haihuwar manzon Allah Ayatollah Ahmad Sayyid Khatami, a hubbaren Imam Rida (AS) inda zai tabao muhimman batutuwa da suka shafi muhimmancin hadin kai tsakanin al'ummar Musulmi.
375967