IQNA

Wani Masanin Addinin Musulunci Dan Danmark Ya Ziyarci Cibiyar Binciken Addini

Bangaren rahoto: Masani kan harkokin addinin Musulunci dan kasar Danmark (Peter Son) ya ziyarci cibiyar gudanar da bincike ta hanyar na'ura mai kwakwalwa kan ilmomin addinin Musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Masani kan harkokin addinin Musulunci dan kasar Danmark (Peter Son) ya ziyarci cibiyar gudanar da bincike ta hanyar na'ura mai kwakwalwa kan ilmomin addinin Musulunci da ke birnin a jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda ya yaba da irin ayyukan da cibiyar take gudanarwa domin fadada bincike kan harkokin addinin Musulunci.
Ya ce a duniyarmu ta yau babar hanya isar da sakon addinin Musulunci ga al'ummomin yammacin turai da ba su da masaniya kan addinin Musulunci da kuma koyarwarsa, ita ce yada shi ta hanyar yanar gizo, kamar yadda wannan cibiya take yi. Kimanin shekaru 27 kenan da Peter son ya karbi addinin Musulunci, ya zuwa yanzu kuma ya musuluntar da mutane sama da tamanin a nahiyar turai.

376003