Bangaren manema labarai:Jalal Bitarafan shi ne bayyana haka cewa: Kudaden da ake bukata na yi wa Hubbaren Imamain Askariyen (AS) ya karu da kashi satin cikin dari.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta nakalto daga majiyar da ke kula da hubbaren cewa kudadaen sake ginawa ko yi masa kwaskwarima ya karu da kashi satin cikin dari.Har ila yau ya kara da cewa tuni aka kamala aikin yi masa kwaskwarima da kashi talatin da bakwai cikin dari yayinda wakilin ma'aikatar yawan bude ido da ziyara ta Iraki ya bayyana cewa: kaso hamsin na ayyukan da suka shafi cikin hubbaren an kamala yayin da dari bias dari na ayyukan wajen hubbaren an kamala.
375924