A wata zantawa da ta hada (Dr. Rahimi) daya daga cikin mambobin kwamitin kula da harkokin ilimi na jami'ar Azad da ke birnin Mashad da kuma kamfanin dillancin labaran Ikna, ya bayyana cewa Imam Rida (AS) daya ne daga limaman gidan manzon Allah, wanda kuma shi da sauran limaman gidan manzo wata mahada ce ta da hada dukkanin musulmi, domin kuwa matsayin ahlul bait matsayi ne da ubangiji ya kebance su da shi, matsayi ne da wani mahaluki ba zai iya kaiwa zuwa gare shi ba, matsayi ne na wakiltar ubangiji a cikin talikansa, da suka hada da mutane da aljannu da tsirrai da dabbobi da dukkanin abun halitta.
Matsayin Imam Rida (AS) matsayi ne na hujjar Allah a bayan kasa, kmar yadda sauran limaman gidan manzo suka da wannan matsayi na hujjojin Allah a kan dukkanin talikai.
375977