IQNA

Kurakuran Cikin Injila Ne Suka Kai Ni Ga Karbar Musulunci

Bangaren siyasa: Kurakuran da ke akwai a cikin injila da na gani da idona, hakan ne ya sani bincike kan Musulunci har na karbe shi a matsayin addini.
(Hosni Mobambala) wani mabiyin addinin kirista da ya karbi addinin Musulunci, ya sheda wa kamfanin dillancin labaran Ikna cewa;, ya karbi addinin Musulunci ne bisa hujja, bayan da ya tabbatar da cewa littafin injila wanda ake amfani da shi a halin yanzu akwai kurakurai da yawa a cikinsa, ga kuma karo da juna da wasu ayoyi ke yi a cikinsa, wanda hakan ke tabbatar da cewa ba shi ne littafin annabi isa ba, domin kuwa littafin annabi Isa ba zai taba kasancewa da kuskure a cikinsa ba, domin kuwa littafinsa littafin ubangiji ne, ubangiji kuma ba ya kuskure, samun kuskure a cikin injila da na karanta ya tabbatar mini da cewa ba littafin ubangiji ba ne, yayin da na samu kur'ani dauke da amsoshi da dan adam ke bukata ba tare da wani kuskure ba, wannan ne ya kai ni ga musulunta.

376023