Bangaren kasa da kasa: Wasu daga cikin malaman addini daga kasar Saudiyya sun ziyarci malaman addini na kasar Labanan, daga cikin wadanda suka gana da su har da Amir Qablan da kuma Allamah Fadlollah.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Almostaqbal) ta kasar Labanan cewa; wasu daga cikin malaman kasar Saudiyya daga birnin Damam sun kai wata ziyara a kasar Labanan, inda suka zanta da wasu manyan malaman addini na kasar, da suka hada da Abdulamir Qablan da kuma Sayyid Fadlollah.
Ofishin Sayyid Muhammad Hosseini Fadlollah daga birnin Beirut ya habarta cewa; ziyarar da malaman saudiyya suka kai kasar Labanan tana tattare da gagarumin muhimmanci, domin kuwa ziyarar ta zo da nufin kara karfafa hadin kai tsakanin al'ummar musulmi, domin kuwa wannan shi ne babban abin da al'ummar musulmi suke kishirwarsa, kamar yadda su ma malaman da ke cikin tawagar malaman Saudiyya suka yaba da irin kyakkyawar tarba da suka samu daga malaman Labanan.
376916