IQNA

An Bayar Da Horo Kan Sanin Matsayin Ma'aiki (SAW) A Brazil

Bangaren kasa da kasa: Cibiyar kula da yada masaniya kan matsayin ma'aiki (SAW) ta gudanar da wani shiri na bayar da horo kan sanin matsayin manzon Allah(SAW) a kasar Brazil.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Al-shaq Ausat) cewa; Cibiyar kula da yada masaniya kan matsayin ma'aiki (SAW) ta gudanar da wani shiri na bayar da horo kan sanin matsayin manzon Allah(SAW) a kasar Brazil. Rahoton ya ci gaba da cewa cibiyar ta bayar da horon ne ga wasu daga cikin musulmin kasar, da suka hada da limamai da kuma malamai a makarantu, adadin wadanda suka samu horon ya kai mutane 120. Shugaban cibiyar (Khalid Bin Abdulrahma Alshai) ya bayyana cewa; babbar manufar bayar da horon ita ce samar da wasu mutane wadanda suke da cikakkiyar masaniya da za su iya bayar da jawabin wajen gamsar da mutanen kasar Brazil, wadanda ba musulmi ba, wadanda ba su da masaniya kan manzon Allah ballantana sakon da ya zo da shi domin tseratar dad an adam daga duhun jahilci.

376901