Bangaren kasa da kasa: A daidai lokacin da aka fara gudanar da tarukan makon hadin kai da tarukan murnar maulidin manzon Allah(SAW) an gudanar da taron maulidi a da ya hada mabiya mazhabar shi'a da kuma 'yan sunna a kasar Iraki.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Al-dastur) da ake bugawa akasar Jordan cewa; A lokacin da aka fara gudanar da tarukan makon hadin kai da tarukan murnar maulidin manzon Allah(SAW) an gudanar da taron maulidi a da ya hada mabiya mazhabar shi'a da kuma 'yan sunna yankin (Azamiyya) da ke arewacin kasar Iraki. Taron ya samu halartar dimbin mutane daga sassa daban-daban na kasar Iraki, da suka hada dukkanin bangarorin sunna da shi'a, kamar yadda taron ya samu halartar malaman addini gami da 'yan siyasa, da kuma jami'an gwamnati, daga cikin manyan jami'an gwamnatin da suka halarci wannan taron maulidi kuwa har da Tarik Hashemi, mataimakin shugaban kasar Iraki.
Babbar manufar shirya wannan taron maulidi ita ce hada kan al'ummar musulmi nakasar Iraki da suke hada sunna da shi'a.
376925