IQNA

Cibiyar Agaji Ta Musulmi Ta Kai Taimako Ga Asibitin Kiritoci A Ranar Maulidi

14:32 - March 12, 2009
Lambar Labari: 1755286
Bangaren kasa da kasa: A kokarin da wata cibiyar musulmi a kasar Malawi take yi wajen karfafa zaman lafiya tsakanin al'ummomin musulmi da kirista, ta kai taimako ga wani asibitin kirista a ranar Maulidin manzon Allah(SAW)
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin (Islam online) cewa; wata cibiyar musulmi a kasar Malawi a kokarin da take yi wajen karfafa zaman lafiya tsakanin al'ummomin musulmi da kirista, ta kai taimako ga wani asibitin kirista a ranar Maulidin manzon Allah(SAW) inda ta raba wasu kayyakin aiki, da suka hada na'urori na zamani gami da magunguna gadaje barguna da dai sauransu. Shugaban cibiyar Lilu Najwa ya sheda wa wasu manema labarai cewa; babbar manufar hakan ita ce kara karfafa dankon zumuntaka da fahimtar juna tsakanin al'ummomin musulmi da na mabiya addinin kiritsa a kasar Malawi, ya ce ta wannan hanyar kuma za su iya samun damar bayyana wa mabiya addinin kirista matsayin ma'aiki (SAW) wanda ake gudanar da tarukan tunawa da lokacin haihuwarsa a ko'ina cikin fadin duniya, musamman ma a kasashen musulmi.

376763



captcha