IQNA

Musulmin Moritious Sun Gudanar Da Taron Maulidin Manzo (SAW)

14:36 - March 12, 2009
Lambar Labari: 1755291
Bangaren kasa da kasa: Musulmin tsibirin Moritious sun gudanar da taron maulidin manzon Allah(SAW) tare da halartar dubban mutane daga bangaren kungiyoyin musulmi da ma na siyasa gami dam asana.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Allafrica) cewa; Mabiya addinin musulunci da ke tsibirin Moritious sun gudanar da taron maulidin manzon Allah(SAW) tare da halartar dubban mutane daga bangaren kungiyoyin musulmi da ma na siyasa gami dam asana, rahoton ya ci gaba da cewa; taron maulidin ya samu halartar manyan jami'an gwamnati, da suka hada da Pira ministan kasar Ram Golam, wanda ya gabatar da jawabi a wajen taron, inda ya bayyana cewa taron maulidi taro ne na hadin kan al'umma, kuma zai yi amfani da wannan damar wajen kiran hadin kan kasa da al'umma kamar yadda manzon musulunci (SAW) ya koyar.
Daga karshe ya taya dukkanin al'ummar musulmin duniya murnar zagayowar wannan lokaci mai albarka.

376691
captcha