Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Kuwait cewa; A yau ne za a fara gudanar da zaman tattaunawa tsakanin Japan da kuma kasashen musulmi a birnin Kuwait, wanda ma'aikatar kula da harkoki da al'adun musulunci ta kasar ta shirya, inda za su tattauna muhimman batutuwa da suka shafi bangarorin biyu.
Ministan ma'aikatar kula da harkokin addini da al'adun musulunci a kasar Kuwait (Nuwaf Ahmad Jabir Al-sabah) ya bayyana cewa; babbar manufar gudanar da wannan taro da za a fara a yau ita ce; samara da wasu hanyoyi da bangarorin biyu za su ci moriyar junansu, bisa la'akari da muhimmancin da suke da shi a matsayi na yankuna da ma matsayi na kasa da kasa, ya ce ko shakka babu kyattata dangantaka tsakanin kasashen musulmi da Japan na tattare da alfanu ga dukkanin bangarorin biyu.
376529