IQNA

An Buga Tare Yada Littafin (Lura A Cikin Ayoyin Kur'ani) A Faransa

13:15 - March 16, 2009
Lambar Labari: 1755726
Bangaren kasa da kasa: An buga tare da yada wani littafi mai suna (Lura a cikin ayoyin kur'ani) a kasar Faransa, wanda cibiyar (Grasset) ta buga a cikin harshen Faransanci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Al-bawabah) cewa; An buga tare da yada wani littafi mai suna (Lura a cikin ayoyin kur'ani) a kasar Faransa, kuma madaba'antar cibiyar Grasset ita ce ta buga wannan littafi a cikin harshen Faransanci, wanda wasu musulmi 'yan asalin kasar Masar mazauna kasar Faransa suka rubuta, da nufin kara fadakar da mai karatun littafin dalilai na tarihi da wahayi da ke cikin kur'ani bisa mahanga ta gaskiya. Wasu daga cikin masana musulmi suna ganin cewa ya zama wajibi a kara fadada fahimtar da sauram mutane ma'anonin kur'ani, musamman ma na kasashen turai, wadanda ba su da masaniya kan kur'ani da koyarwarsa, kuma suna da masaniya wadda ba ta gaskiya ba, sakamakon parpagandar karya da batunci da wasu ke yi kan kur'ani da musulmi da koyarwar addininsu, wanda yake dauke da madaukakan manufofin na shiryar dad an adam.

377457






captcha