IQNA

Babu Wani Sautin Kur'ani Da Ke Natsar Da Mutum Kamar Na Mustafa Isama'il

13:14 - March 16, 2009
Lambar Labari: 1755727
Bangaren kur'ani: Daya daga cikin fitattun makaranta kur'ani da duniya ya bayyana cewa; babu wani sautin karatun kur'ani da ke natsar da zuciya kamar kira'ar Mustafa Isma'il.
A cikin wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da kuma makarancin nan na kasar Iran (Hashem Roghani) wanda daya ne daga cikin fitattun makaranta kur'ani da duniya ya bayyana cewa; babu wani sautin karatun kur'ani da ke natsar da zuciya kamar kira'ar Mustafa Isma'il, makarancin ya ci gaba da cewa a duk lokacin da Mustafa Isma'il yake karatun kur'ani yana sa mai sauraronsa cikin wani yanayi na natsuwa da tuna ubangiji, wanda kuma a lokaci guda yana jefa mai sauraronsa cikin tunanin ma'anonin ayoyin kur'ani da yake karantawa tare da yin la'akari da su kamar yadda ake bukatar mai sauraro ya kasance, wannan na daya daga cikin abubuwan da suka banbanta shi da sauran masu karatun kur'ani.

374330
captcha