IQNA

Ban Ki-Moon Ya Nuna Damuwa Dangane Da Halin Da Gaza Ke Ciki

15:46 - March 14, 2009
Lambar Labari: 1755861
kasa da kasa: Sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki- Moon ya nuna matukar damuwa dangane da halin da Bangaren al'ummar Gaza ke ciki.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran SANA cewa; Sakatare janar na majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon ya nuna matukar damuwa dangane da halin da al'ummar Gaza ke ciki, inda ya kirayi Isra'ila da ta gaggauta janye killacewar da take yi wa yanzkin Zirin Gaza ba tare da wani bata lokaci ba. A cikin wata wasika da ya aike wa masu taron birnin Alkahira, ya bayyana cewa ya zama wajibi a cimma matsaya kan makomar Gaza, domin kuwa al'ummar yankin suna cikin wani mawuyacin hali, kuma ya zama wajibi a cimma matsaya dangane da batun bude wuta, kuma kirayi Isra'ila da ta janye killacewar da take yi wa yankin Gaza cikin gaggawa, domin a cewarsa hakan na ci gaba da jefa al'ummar yankin cikin mawuyacin hali na rayuwa.

377398
captcha