IQNA

Za A Kafa Kwamitin Limaman Masallatai A Faransa

Bangaren kasa da kasa: Shugaban kwamitin musulmi na garin (Droncy) da ke arewacin kasar Faransa (Hassan Shalgomi) ya bayyana cewa za a kafa kwamitin limaman masallatai da ke kasar Faransa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Faransa(AFP) cewa; Shugaban kwamitin musulmi na garin (Droncy) da ke arewacin kasar Faransa (Hassan Shalgomi) ya bayyana cewa za a kafa kwamitin limaman masallatai da ke kasar Faransa, ya bayyana hakan ne a wani taro da kwamitin hadin gwiwa tsakanin musulmi da yahudawan kasar Faransa (Val-de- Marne) ya gudanar, inda ya bayyana cewa kafa kwamiti irin wannan yana da matukar muhimmanci, domin kuwa a cewarsa ta hanyar kafa wannan kwamiti ne za a iya sanin adadin limamai da suke kasar faransa baki daya, kamar yadda ta hanyar hakan ne za a iya sanin matsalolinsu tare da daukar matakan da suka dace wajen warware su. Ya kara da cewa daga cikin abin da za su kara karfafa gwiwar limamai kansa har da fadakar da sauran mutane wadanda ba mabiya addinin musulunci ba ne, domin su fahimci hakikanin addinin musulunci ba addini ne na ta'addanci ko tashin hankali ba kamar yadda ake nuna musu.

377421