Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (Ma'a) cewa; An kawo karshen gasar karatun kur'ani da dalibai 'yan makaranta suka gudanar a yankin Zirin Gaza, inda dalibai na makarantun gaba da firamare suka gudanar da karatuka, da hakan ya hada da hardar kur'ani baki daya, da kuma hardar juzu'I sha biyar zuwa kasa, kamar yadda a bangare guda kuma an gudanar da gasar karatun kur'ani da kira'ar tartili, gami da tajwidi, wato kiyaye ka'idojin karatun kur'ani mai tsarki. Cibiyar kula da karatun kur'ani a Gaza it ace ta shirya wannan gasa, inda shugaban cibiyar ya bayyana cewa babbar manufar shirya wannan gasa ita ce karfafa yara masu tasowa da ma matasa wajen karatun kur'ani da hardarsa, inda kuma ya zuwa yanzu an samu gagarumin ci gaba a dukkanin fuskokin biyu, ya ce hakan zai ba matasa dammar koyon karatun kur'ani tare da kiyaye ka'idojin karatunsa yadda ya kamata, kamar yadda hakan zai taimaka musu wajen hardar kur'ani.
377428