IQNA

An Bukaci Majalisar Dinkin Duniya Da Ta Hana Wulakanta Addinai

15:45 - March 14, 2009
Lambar Labari: 1755866
Bangaren kasa da kasa: Kasashen musulmi sun aike da wata wasika zuwa ga kwamitin kare hakkin bil'adama na majalisar dinkin duniya, inda suka bukaci kwamitin da ya kafa dokar hana wulakanta addinai.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (AFP) na kasar faransa cewa; Kasashen musulmi sun aike da wata wasika zuwa ga kwamitin kare hakkin bil'adama na majalisar dinkin duniya, inda suka bukaci kwamitin da ya kafa dokar hana wulakanta addinai, inda suka bayyana cewa ci gaba da wulakanta addinai da aka safkar daga sama da ake ci gaba da yi a kasashen turai ya wuce haddi, kuma hakan tamkar neman tsokanan ne ga mabiya addinan. Bayanin ya ci gaba da cewa hada addinin muslunci da ayyukan ta'addanci da wasu bangarori ke yi ba adalci ban e ga addinin musulunci da kuma musulmi. Kasar Pakistan da ke wakiltar kasashen musulmi mambobi a OIC, ta nuna matukar damuwarta kan ci gaba da zane-zanen batunci ga manzon Allah (SAW) da ake yi a wasu kasashen yammacin turai, inda ta bayyana cewa ba 'yancin bayyana ra'ayi ban e wulakanta addinin wasu.

377432
captcha