IQNA

An Fara Taro Kan Fikihun Musulunci A Kasar Turkiya

Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da zaman taro na kasa da kasa kan fikihun musulunci a birnin Istanbul na kasar Turkiya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Mohit) cewa; an fara gudanar da zaman taron kan fikihun musulunci a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, wanda ke samun halartar malamai dam asana gami da malaman jami'oi daga kasashen duniya daban-daban. Babbar manufar gudanar da taron ita ce tattaunawa dangane da muhimman batutuwa da suka shafi mas'aloli na fikihu, wadanda suke bukatar dogon bahasi domin samara da matsaya guda da dukkanin bangarori za su amince da ita bisa dalilai na shari'a, bisa la'akari da banbancin zamani da aka samu, wanda hakan ya tilasta malamn fikihu sake yin nazari kan yadda za a aikata wasu hukunce-hukuncen addini, da kuma samara da wasu hukunce-hukuncen kan wasu lamurra da suka bijro daga bisani, musamman ma a wannan zamani da muke ciki, wadanda fikihu bai tabo suba a lokutan baya. Yanzu haka dai manyan malamai na ci gaba da gudanar da wannan taro da kuma yin bahasi kan muhimman mas'aloli na fikihu da ke bukatar yin nazari kan yadda za a aikata su a wannan zamani.

377465