Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Ayatollah Mohammad Ali Taskhiri Sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin musulunci ya bayyana cewa manufar gudanar da taron makon hadin kai a mahangar Imam Khomeni(RA) ita ce dawo da karfin musulmi da suka rasa, malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabin bude taron makon hadin kai yau a babban ginin tsohuwar majalisar shawarar musulunci ta Iran. Taron wanda yake samun halartar manyan malamai da masana daga sassa daban-daban na duniya, ya yi tsokaci kan muhimman mas'aloli na hadin kai tsakanin al'ummar musulimi, inda dukkanin mahalarta taron suka yi nuni da wajabcin da ke tattare da hadin kai tsakanin al'musulmi, tare da nuna farinciki kan ci gaban da aka samu ta wannan fuska tun bayan da marigayi Imam Khomeni ya assa wanna mako na hadin kan al'ummar musulmin duniya, wanda ya zo daidai da ranakun murnar tunawa da haihuwar manzon Allah.
377457