Kamfanin dillancin labaran ikna ya habarta cewa; da safiyar Juma'a 23 ga watan Esfand, an fara gudanar da taron makon hadin kai tsakanin al'ummar musulmi a birnin Tehran, sakatarn cibiyar kusanto da mazhabobin musulunci Ayatollah Mohhamd Ali Taskhiri, ya gabatar da jawabin bude taro, inda ya bayyana cewa manufar taron na makon hadin kai shi ne kara fadada fahimtar juna tsakanin al'ummar musulmi. A nasa bangaren sakataren kwamitin kula da harkokin ilimi na cibiyar ya bayyana cewa; taron na bana wanda shi ne irinsa na 22 da ake gudanarwa, yana samun halartar malamai da fitattun masana daga kasashe daban-daban na duniya, inda suke gabatar da jawabai kan mahangarsu dangane da muhimmancin da ke tattare da hadin kai tsakanin al'ummar musulmi.
377415