Bangaren kasa da kasa: Mulkin kama karya da akidar yahudancin sahyuniya su manyan ummul haba’isin matsalolin da musulmi ke fama da su, da hakan ya lizimta wa musulmi shiga hayyacinsu tare da hada kansu.
Kamfanin dillancin lbaran Ikna ya habarta; limamin masallacin juma’a na birnin Washington na kasar Amurka ya bayyana cewa; : Mulkin kama karya da akidar yahudancin sahyuniya su manyan ummul haba’isin matsalolin da musulmi ke fama da su, da hakan ya lizimta wa musulmi shiga hayyacinsu tare da hada kansu.
Malamin ya bayyana hakan ne a wurin taron makon hadin kai da aka gudanar a nan birnin Tehran. Ya ci gaba da cewa al’ummar muslmi na bukatar hadin kai a halin fiye da sauran lokuta da suka gabata, domin kuwa suna fuskantar danniya a siyasance da fuskar tattalin arziki da ma soji, wanda hadin kansu shi ne babbar mafita gare su.
378016