IQNA

Kwamitin Bincike Kan Yanayin Gaza Ya Gudanar Da Zama

15:03 - March 16, 2009
Lambar Labari: 1756475
Bangaren kasa da kasa: Kwamitin da kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta kafa domin gudanar da bincike kan yanayin da al’ummar Gaza ke ciki da kuma sanin irin bukatun da suke da su na gaggawa ya gudanar da zama.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran SANA cewa; Kwamitin da kungiyar hadin kan kasashen larabawa ta kafa domin gudanar da bincike kan yanayin da al’ummar Gaza ke ciki da kuma sanin irin bukatun da suke da su na gaggawa ya gudanar da zama. Rahoton ya ci gaba da cewa kwamitin ya gudanar da zaman ne domin sanin halin da al’ummar Gaza ke ciki musamman ma kananan yara da mata, wadanda sun e suka fi shiga cikin mawuyacin hali sakama sakamakon yakin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kaddamar kan yankin a lokutan baya, wanda kuma har yanzu bas u gushe suna fuskantar wahalhalun rayuwa sakamakon hakan ba.


378044
captcha