IQNA

Za A Gudanar Da Wani Zama Na Musamman Kan Palastinu

15:00 - March 16, 2009
Lambar Labari: 1756480
Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da zama kan batun apalstinu tsakanin wakilan kasashen Labanan da na Iran gami da palastinu a gefen taron makon hadin kai.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; za a gudanar da zama kan batun apalstinu tsakanin wakilan kasashen Labanan da na Iran gami da palastinu a gefen taron makon hadin kai, inda babban malamai kuma mai bayar da fatawa a birnin Qods (sheikh Ikramah Sabri) zai jagoranci zaman, tare da sakataren cibiyar kusanto da mazhabobin Musulunci (Mohammad Hossein Tabrian) da kuma wasu daga cikin malamai da da suka halarci taron makon hadin kai da aka kammala a birnin Tehran, wanda ya yi dubi kan irin muhimmancin da ke tattare da hadin kan al'ummar musulmi, domin fuskantar muhimman mas'alolin da suke ci musu tuwo a kwarya.

378074





captcha