IQNA

Sarkin Saudiyya Ya Karbi Kyautar Kur'ani Mai Rubutun Zinari

14:59 - March 16, 2009
Lambar Labari: 1756482
Bangaren kasa da kasa: Jakadan kasar Rasha a kasar Saudiya (Benyamin Bobov) ya bayar da kyautar kur'ani mai rubutun zinariya ga sarkin kasar Saudiyya Abdllah Bin Abdulaziz.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na (Qods) cewa; Jakadan kasar Rasha a kasar Saudiya (Benyamin Bobov) ya bayar da kyautar kur'ani mai rubutun zinariya ga sarkin kasar Saudiyya Abdllah Bin Abdulaziz, domin bayyana mahangar gwamnatin Rasha kan muhimmancin da ke tattare da tattaunawa kan addinai, inda Rasha take girmama irin matakan da kasashen musulmi suke dauka na kara fadada fahimtar juna tsakaninsu da sauran addinai, wanda hakan ke tabbatar da cewa ci gaba da yin hakan zai kawo karshen duk wani rashin fahimtar juna da ke akwai tsakanin addinai, tare da kawo zaman lafiya da son juna a tsakanin mabiya a ddinan a fadin duniya.

378097
captcha