IQNA

An Fitar Da Littafi Kan Lamurran Matasa A Duniyar Musulmi

14:58 - March 16, 2009
Lambar Labari: 1756495
Bangaren kasa da kasa: An fitar da wani littafi kan lamurran matasa a duniyar musulmida, wanda cibiyar kula da ilimida al'adun kasashen musulmi ta buga kuma ta dauki nauyin yadawa.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga jaridar (Al-riyad) da ake bugawa a kasar Saudiyya cewa; an fitar da wani littafi kan lamurran matasa a duniyar musulmida, wanda cibiyar kula da ilimida al'adun kasashen musulmi ta buga kuma ta dauki nauyin yada shi, kungiyar ta dauki nauyin buga wannan littafi net un bayan zaman da ta gudanar a birnin Tunis na kasar Tunusia a cikin watan Nuwamban shekara ta 2008 da ta gabata.
A cikin littafin an kawo makalolin masana da malaman jami'oi gami da marubuta a kasashen musulmi, wadanda suka tabo muhimman batutuwa da suka shafi matasa a duniyar musulmi, da nufin sama musu hanya mafi dacewa da koyarwar addinin Musulunci wajen warware matsaloli da dama da suke fuskanta a cikin rayuwarsu, da hakan ya hada da matasa musulmi da suke rayuwa a kasashe wadanda ban a musulmi ba, musamman ma kasashen turai, da yadda ya kamata su rika gudanar da lamurransu ba tare da sun sabawa hukunce-hukunce ko koyarwar addininsu ba.

378154
captcha