IQNA

Makiya Na Kulla Makircin Rikidewar Sabani Ilimi Ya Koma Na Kabilanci Da Akida

15:14 - March 16, 2009
Lambar Labari: 1756543
Bangaren tunani:makiya na ta fadi tashin ganin sun kulla makircin rikidewar rikicin ilimi ya koma na akida da kabilanci domin su cimma burinsu munana.
Hujjatul Islam da musulmi Ali Rajabi shugaban Hauza da jami'a a wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna dangarne da hadin kan musulmi a tarihin musulunci ya bayyana cewa: mutum na farko day a kaddamar da wannan mataki mai muhimmanci na hada kan musulmi shi ne Manzon rahama Tsira da amincin Allah ya Tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarka sai kuma Imam Ali (AS) bayan kaurar manzon Allah (SWA) amma a tsawon tarihi makiya babu wani lokaci da suka daina kulla makircin rarraba kawunan musulmin duniya.

376621
captcha