IQNA

Sakataren Kungiyar Hadin Kan Musulmi Ta OIC Ya Isa Gaza

12:37 - March 17, 2009
Lambar Labari: 1756714
Bangaren kasa da kasa: Sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC (Ikmal Ihsan Auglo) ya isa Gaza, domin duba irin barnar da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi a yankin a hare-haren da ta kaddamar kan al'ummar yankin a lokutan baya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (World Bulletin) cewa; Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC (Ikmal Ihsan Auglo) ya isa Gaza, domin duba irin barnar da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi a yankin a hare-haren da ta kaddamar kan al'ummar yankin a lokutan baya, bayan isarsa yankin Gaza sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ya gana da jami'an halastacciyar gwamnatin Palastinu karkashin jagorancin Hamas, dangane da yadda za a sake gina yankin zirin Gaza bayan da haramtacciyar gwamnatin yahudawa ta ragargaza shi.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai ya nuna jin dadinsa matuka dangane da tattaunawar da kungiyoyin palastinawa suke yi, da nufin kaiwa ga batun kafa gwamnatin hadin kansa da za ta hada dukkanin bangarori.

378412












captcha