IQNA

Za A Gane Musulamai Ne Ta Hanyar Tabbatar Hadin Kansu

12:38 - March 17, 2009
Lambar Labari: 1756715
Bangaren kasa da kasa: Bukatuwa zuwa ga hadin kai, aiki tare, hadin gwiwa tsakanin musulmi a cikin lamurransushi ne babban abin da zai kara fito da hakikanin surar musulmi da Musulunci a wajen sauran al'ummomin duniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a cikin wani bayani da tsohon shugaban kasar Afganintan Burhanuddin Rabbani ya gabatar a wajen taron makon hadin kai ya bayyana cewa; bukatuwa zuwa ga hadin kai, aiki tare, hadin gwiwa tsakanin musulmi a cikin lamurransushi ne babban abin da zai kara fito da hakikanin surar musulmi da Musulunci a wajen sauran al'ummomin duniya, ya kara da cewa al'ummar musulmi ta kasar Afganistan ta tabbatar da hakan a aikace, a lokacin da rundunar tsohuwar tarayyar Soveit ta nemi mamaye kasar Afganistan tare da neman yin wani sabon mulkin mallaka a kanta, a lokacin da musulmin Afganistan suka hada karfi da karfe sun fatattaki dakarun tsohuwar tarayyar Soveit daga cikin kasarsu. Ya ce wannan misali ne da al'ummar musulmi ta duniya za ta dauka, idan muka hada kai babu wanda zai iya kutsawa tsakaninmu balntana har ya ga inda zai iya rusa mu.

378466

captcha