Kamfanin dillancin labaran ikna ya habarta cewa; a cikin wani bayani da ya gabatar a wajen rufe taron makon hadin kai limamin birnin Najful asharaf (Sadruddin Kubanchi) ya bayyana cewa; tabatar hadin kai tsakanin al'ummar musulmi ba wai kawai wani lamari ne na al'adu ba, a'a hakan na bukatuwa zuwa ga aikin hadin gwiwa tsakanin musulmi, ya ci gaba da cewa a cikin 'yan lokutan da suka gabata, al'ummar Iraki sun nuna wa sauran al'ummomi cewa; yin aiki tare shi ne babban kashin bayan samun kowace nasara, inda suka gudanar da zabuka a cikin tsari ba tare da hakkin wani bangare ya saraya ba, wanda hakan ke tabbatar da wani sha'ani mai girma da ya afku a tarihin kasar, domin kuwa zabukan sun hada mabiya mazhabar shi'a da 'yan sunna baki daya, kuma kowannensu na 'yancin ya zabi wanda yake so daga daya bangaren ba tare da wata matsala ba.
378506