IQNA

Masu Koyi Da Kira'ar Mustafa Isama'il Ba Su Iya Kamo Kafarsa Ba

12:48 - March 17, 2009
Lambar Labari: 1756719
Bangaren kur'ani: Wani daya daga cikin fitattun makaranta kur'ani na kasa da kasa ya bayyana cewa; wadanda suka fi kowa shahara wajen yin koyi da salon karatun kur'ani na Mustafa Isma'ail ba su iya kamo kafarsa ba.
A cikin wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da wani fitaccen makarancin kur'ani na kasar Iran (Saleh Athari Fard) ya bayyana cewa; wadanda suka fi kowa shahara wajen yin koyi da salon karatun kur'ani na Mustafa Isma'ail ba su iya kamo kafarsa ba, domin kuwa a cewar makarancin Mustafa Isma'il ya kebantu da wani salo wajen karatun kur'ani wanda babu wanda zai iya yinsa kamarsa sai dai a kwatanta, ya ci gaba da cewa mutum ne da yake daga muryarsa a wasu wurare na musamman, kamar yadda yakan yi kasa da muryarsa a wasu wurare na musamman, kamar yadda yakan jinkirta a wasu wurren, ya ce duk hakan ba wai don ya burge masu saurare ba ne, a' a yak an yi la'akari ne da abin da aya take magana a kansa, wato yanayin da aya take magana akansa sda irin wannan salon zai karanta ta, lamarin da kan jefa masu saurare kai tsaye cikin tunani dangane da ma'anar ayoyin.

374191


captcha