Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a lokacin da aka kawo karshen taron makon hadin kai a birnin Tehran, an gudanar da wani zama na musamman kan batutuwa da suka danganci palastinu, da kuma halin da al'ummar yankin suke ciki, musamman ma dai alummar Gaza da suke cikin halin jiran taimako daga 'yan uwansu musulmi daga sassa na duniya. A yayin gudanar da taron babban sakataren cibiyar ahlul bait ta duniya Muhammad Hassan Akhtari, wanda ya jagoranci zaman kan sha'anin Palastinu ya bayyana cewa; al'ummar palastinu suna da wani bababn nauyi a kan al'ummar musulmi baki daya, kuma hakan na bukatar hadin kai tsakanin al'ummar musulmi kafin safke wannan babban nauyi da ya rataya kan al'ummar musulmi dangane da 'yan uwansu da ke palastinu.
378399