Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a wata zantawa da ya yi tare da manema labarai jim kadan bayan kammala taron makon hadin kai, ministan kula da al'adu na kasar Iran Mohammad Hossein Saffar Herandi ya bayyana cewa; hada baki da makiya Musulunci da wasu daga cikin kasashen muslmin ke yi, na daya daga cikin muhimman matsalolin duniya musulmi. Ya ci gaba da cewa babbar manufar kasashe da ke kiyayya da Musulunci ita ce ci gaba da haifar da baraka da rashin fahimtar juna a tsakanin al'ummar musulmi, domin a iyakacin fahimtarsu, samun hadin kai tsakanin msulmi ba maslaha ce gare su, amma kuma abin ban takaici shi ne yadda wasu daga cikin kasshen musulminnne suka dauki nauyin yi musu aikin da suke bukata na raba kan al'ummar musulmi.
378882