Bangaren kasa da kasa: Ministan harkokin wajen jamhuriyar Musulunci ta Iran Manochehr Mottaki, ya bayyana cewa yin namijin kokari wajen hada kan palastinawa da samun fahimtar juna tsakanin kasashen musulmi da na larabawa nauyi da ya rataya kan shugabannnin kasashen musulmi da na larabawa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a wani taron manema labarai da ministan harkokin wajen Iran Manochehr Mottaki ya gudanar tare da takwaransa na kasar Saudiya jiya a birnin Riyad fadar mulkin kasar ya bayyana cewa; yin namijin kokari wajen hada kan palastinawa da samun fahimtar juna tsakanin kasashen musulmi da na larabawa nauyi da ya rataya kan shugabannnin kasashen musulmi da na larabawa, ya ci gaba da cewa; kasashen Iran da Saudiyya suna da rawar da za su taka wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, da kuma hada kan al'ummar musulmi, kuma nauyi ne da ya rataya kansu da ma sauran dukkanin kasashen musulmi da su tsaya kai da fata wajen kare al'ummomin musulmi da ake zalunta, musamman ma al'ummar palastinu marassa kariya.
A nasa bangaren ministan harkokin wajen kasar saudiyya Sa'udul Faisal ya bayyana cewa; hakika yankin gabas ta tsakiya da ma duniyar musulmi na fuskantar matsaloli masu yawa, wanda kuma warwaresu na bukatar hada karfi da karfe tasakanin dukkanin kasashen yankin da sauran kasashen musulmi, ya yaba wa Iran kan namijin kokarin da ya ce tana yi kan hakan.
378337