IQNA

An Fara Gudanar Da Taron Makon Kur’ani A Algeria

11:24 - March 18, 2009
Lambar Labari: 1757347
Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da taron makon kur’ani a karo na goma a kasar Algeria a safiyar Talata a garin (Darul Imam)
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Elmoujahid cewa; an fara gudanar da taron makon kur’ani a karo na goma a kasar Algeria a safiyar Talata a garin Darul Imam, wanda kuma shugaban kasar ta Algeria Abdulaziz Butaflika shi ne wanda ya fara assasa wannan shiri na makon kur’ani, wanda ma’aikatar kula da lamurran addini ta kasar ta dauki nauyin ci gaba da gudanar da shi a kowace shekara, inda bana shirin ya shiga shekara ta goma. Rahoton ya kara da cewa; taron yana samun halartar masana da manyan jami’an gwamnati, da kuma makaranta kur’ani daga sassa daban – daban na kasar.

379051
captcha