IQNA

Mustafa Isma’il Tauraro Ne Mai Haske Da Samuwar Karatun Kur’ani

11:33 - March 18, 2009
Lambar Labari: 1757348
Bangaren kasa da kasa: Daya daga cikin makaranta kur’ani daga kasar Iran ya bayyana marigayi Mustafa Isma’il a matsayin wani tauraro da ke haske da samuwar karatun kur’ani, a ake samun irinsa da kyar sau daya a cikin shekaru 100.
A cikin wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da makarancin kur’anin nan na kasar Iran da ya shahara ta fuskacin kira’a (Sayyid Mahdi Fatimiyan) ya bayyana cewa; marigayi Mustafa Isma’il wani tauraro ne da ke haske da samuwar karatun kur’ani, da ake samun irinsa da kyar sau daya a cikin shekaru 100, ya ci gaba da cewa yanayin kira’arsa ya sha banban da duk wani mai karatun kur’ani da ya shahara a wannan zamani, domin kuwa hatta malaman da ake kallonsu a matsayin makaranta na wannan zamani da ake komawa zuwa salon kira’arsu, kamar su sheikh Abdulbasit Abdulsamad da dai sauransu, suna girmama sheikh Mustafa Isma’il a matsayin malaminsu da suke komawa zuwa gare shi.

374256

captcha