Bangaren kasa da kasa: Ayatollah Imami Kashani mamba a majalisar fayyace maslahar tsarin musulunci zai jagoranci sallar juma’a ta karshen shekara a birnin Tehran.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Ayatollah Imami Kashani mamba a majalisar fayyace maslahar tsarin musulunci zai jagoranci sallar juma’a ta karshen shekara a birnin Tehran, inda zai tabo muhimman abubuwa da suka faru a cikin wannan shekara musamman wadanda suka shafi duniyar musulmi da kuma jamhuriyar musulunci ta Iran a cikin gida da kuma waje, tare da yin hannuka mai sanda ga al’umma kana bin da ka iya kai ya komo. Rahoton ya kara da cewa mataimakin ministan ilimi na kasa zai gabatar da wani jawabi a wajen sallar juma’a.
379103