IQNA

Za A Iya Isar Da Sakon Kur’ani Ta Hanyar Shirye-Shirye Na Zamantakewa

11:25 - March 18, 2009
Lambar Labari: 1757352
Bangaren fasaha: Shirin sinima da ake gudanarwa a Iran zai iya taka gagarumar rawa wajen isar da sakon kur’ani tare da wayar da kan al’umma kamar yadda ya kamata
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya zanta da daya daga cikin masu gudanar da shirye-shiryen sinima da suka yi fice a kasar Iran (Abdulriza Akbar) inda ya bayyana cewa; shirin sinima da ake gudanarwa a Iran zai iya taka gagarumar rawa wajen isar da sakon kur’ani tare da wayar da kan al’umma kamar yadda ya kamata, ya ce masu gudanar da shirye-shiryen sinima da sauran ayyukan al’adu a Iran, suna taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al’umma dangane da abubuwa da dama da suka shafi rayuwar jama’a ta zamantakewa a addinance, kuma za su iya taka rawa kamar yadda kamata wajen isar da sakon kur’ani a cikin shirye-shiryensu na sinima da suke gudanarwa.

379020






captcha