IQNA

Jami’ar Princeton Ta Bude Dakin Karatun Littafan Musulunci A Internet

Bangaren kasa da kasa: Jami’ar Princeton ta kasar Amurka ta bude wani dakin karatun littafan addinin musulnci ta hanyar internet, inda ta saka littafai 200 ga masu bukatar nazari.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na jami’ar Princeton cewa; jami’ar ta bude wani bangare a shafinta domin gudanar da bincike kan addinin musulunci, inda ta saka littafai kimanin 200 ga masu bukatar yin nazari, kuma za ta kara fadada bangaren da kebe domin gudanar da bincike da yin nazari kan addinin musulunci. Bayanin ya kara da cewa jami’ar ta shirya hakan tun a cikin shekara ta 2005, amma ba aiwatar da shirin nata ba sai a cikin wannan shekara, kamar yadda ta hanyar hakan jami’ar za ta iya bayar da dama ga masu gudanar da bincike da su yi amfani da shafin nata wajen fitar da littafan da suke bukata, amma hakan zai yuwu ne kawai bayan tuntubar bangaren da ke kula shafin internet na jami’ar, tare da sanin dalilin hakan.

379014