IQNA

Gwamnatin Nepal Ta Amince Da Kare Hakkokin Musulmi A Hukumance

11:30 - March 18, 2009
Lambar Labari: 1757356
Bangaren kasa da kasa: Gwamnatin kasar Nepal ta amince a hukumance da batun kare hakkokin musulmi a kasarta, biyo bayan rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakaninta da babban kwamitin da ke kula da harkokin musulmin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (Himalayan Times) cewa; gwamnatin kasar Nepal ta amince a hukumance da batun kare hakkokin musulmi a kasarta, biyo bayan rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakaninta da babban kwamitin da ke kula da harkokin musulmin kasar, inda aka saka wannan yarjejeniya a cikin ayar doka ta shida da ke cikin kundin tsarin mulin kasar, da ke nuni da cewa kundin tsarin mulkin kasar bai san da zaman addinin musulunci ko mabiyansa a kasar ba, amma wannan yarjejeniya da gwamnati ta kulla da kwamitin musulmin kasar ya samya ta canja wannan ayar doka, inda yanzu haka gwamnatin ta kafa nata kwamitin domin kare hakkokin musulmin kasar a hukumance.

379070

captcha