IQNA

Musulmi Suna Bin Fatawar Malamansu Kan Batun Hadin Kai

11:29 - March 18, 2009
Lambar Labari: 1757358
Bangaren fikra: A yau an wayi gari akasarin musulmi suna bin fatawowi malamansu ne wajen batun hadin kai, yayin da wasu daga cikinsu suke kallon hakan a matsayin wajibi ne da baya bukatar fatawa.
A cikin wata zantawa da kamfanin dillancin labaran Ikna ya yi tare da wakilin jagoran juyin juya halin musulunci ta fuskacin isar da sako a wajen kasar Mohammad Reza Nurullahiyan ya bayyana cewa; akasarin musulmi suna bin fatawowi malamansu ne wajen batun hadin kai, yayin da wasu daga cikinsu suke kallon hakan a matsayin wajibi ne da baya bukatar fatawa, ya ce a duk lokacin da batun hadin kai da neman sulhu tsakanin musulmi ya taso babu batun neman fatawa a cikinsa, domin kuwa hadin kan al’ummar muslmi shi ne nasararsu, musamman ma a wannan lokaci da al’ummar musulmi ke fuskantar matsaloli da dama musamman ma daga makiyan addini da suka hada da yahudawan sahyuniya. Ya ce hadin kai tsakanin musulmi wajibi ne da ya rataya kansu baki daya.

378746

captcha